An bude taron 'yan jaridu na Deutsche Welle
May 27, 2019Daga ranar Litinin 27 zuwa Talata 28 ga watan Mayu, tashar Deutsche Welle na karbar bakuncin wakilan kafofin yada labaru daga sassa dabam-dabaM na duniya a nan birnin Bonn domin babban taron kafofin yada labaru na Global Media Forum karo na goma sha biyu.
Jigon muhawara a taron shi ne sauyin karfin iko. A wurare da dama dangantaka tsakanin kafofon yada labaru da fannin siyasa da kuma zamantakewar al'umma ya fuskanci sauyin matsayi da ma tangarda a wasu lokutan sakamakon sauyi na cigaban fasahar zamani na
Verica Spasovska jagorar tsare-tsaren gudanar da taron na Global Media Forum Ta ce: '' Tsare-tsaren da aka yi a bana sun dara na shekarun baya domin a wannan shekarar muna da tsare-tsare ga dukkan mahalarta taron, sannan a rana ta uku da aka shirya wa wasu mutanen da aka gayyato wanda ma'aikatar harkokin waje za ta dauki dawaniya, kuma a wannan karon mun shirya taruka dabam-dabam sabanin shekarun baya inda galibi aka yawaita tarukan babban zaure. Akwai kuma tarukan ganawa mai armashi da aka shirya da 'yan jaridu"
'Yancin fadar albarkacin baki ya yi rauni.
A wani tsokaci da ya yi shugaban tashar DW Peter Limbourg ya ce babakere da nuna tasiri kan samun bayanai ya zama abin dogaro na nuna karfin iko yana mai cewa " 'Yan siyasa na kowane bangare masu akidar nuna cewa sune na talakawa da kuma ke nuna wa jama'a cewa 'yan Boko da ke cikin gwamnati sun mayar da talakawa saniyar ware suna yin barazana ga hadin kan Turai."
Limbourg ya ce a lokaci guda kuma wadannan 'yan siyasa suna yada sakonninsu tare da kokarin mallake kafofin yada labaru mallakar gwamnati ko kuma yada bayanai marar inganci a kafofin sada zumunta. A takaice dai a cewar Limbourg yancin fadin albarkacin baki ya yi rauni.
Babban manufar wannan taron na kwanaki biyu shi ne jawo hankali ga muhimman ginshikan da suka haifar da wannan sauyi.
Shugaban kasar Jamus Frank Walter Steimmeier ya gabatar da jawabin bude taro da aka yada ta kafar video.
Bayan wannan mahalarta taron za su tattauna a kan yadda yanayin kafofin yada labarai ke sauyawa tare da yin tsokaci a kan wuraren da suke fuskantar hadari da kuma inda ake da damammaki.