1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shekara shekara na asusun IMF a birnin Washington

Mohammad Nasiru AwalOctober 20, 2007

Kasashe masu tasowa na ƙorafi da rashin ba su cikakken wakilci a cikin IMF.

https://p.dw.com/p/BvQK
Ministan kuɗin Jamus Peer Steinbrück
Ministan kuɗin Jamus Peer SteinbrückHoto: AP

Kasashe masu tasowa wadanda suka kasance kashin bayan bunkasar tattalin arzikin duniya a cikin shekarun bayan nan na korafin cewa ba su da cikakken wakilci daidaiwa daidai da takwarorinsu na kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya a cikin asusun na IMF. Kasashen sun nuna rashin gamsuwa atre da cewa ba abin karbuwa ba ne ga abin da suka kira tafiyar hawainiya da ake yi na yiwa asusun kwaskwarima. Kasashen wadanda kr da rinjaye a yawan membobin IMF ba su da wani karfi a cikin ayyukansa. Tun gabanin bude taro na birnin Washington kungiyar kasashe masu tasowa wato G24 ta jaddada kiranta na ba ta babbar murya da wakilci bisa manufa ta demokiradiya. Mataimakin ministan tattalin arzikin kasar Argentina Oscar Tangelson wanda ya jagoranci wani taron kungiyar ta G24 ya ce kungiyar ta dauki wani mataki na cimma yarjejeniya ta bai-daya akan ka´idar raba yawaan kurti´u a cikin IMF. Asusun wanda aikinsa shi ne daidaita harkokin kudi a duniya yanzui shi kansa yana gwagwarmaya daidaita kasafin kudinsa. Yayin da wasu kasashe suka biya basussukan su wasu kuwa korafi suke yi game da tsauraran sharuddan asusun. Hakazalika asusun na gudanar da wannan taro akan halin da tattalin arzikin duniya ke ciki a daidai lokacin da ake fama da matsalolin kasuwannin hada-hadar kudi na duniya. Ministan kudi na tarayyar Jamus, Peer Steinbrück ya yi nuni da cewa ko da yake ba´a shawo kan matsaloli a bankunan ba da rance na kasar Amirka amma an fara ganin alamu sararawar mawuyacin hali da suka shiga ciki.

Steinbrück:

Steinbrück ya ce “Ko shakka babu matsalolin kudi a kasar Amirka suna mummunan tasiri a kasashen Turai. A da ma mun taba samun tashin darajar kudin Euro akan dala. Ko da yake tattalin arzikin Jamus ya dogara ne akan kayakin da take sayarwa a ketare, amma ba canjin da ake samu a harkar musayar takardun kudaden bai shafarmu sosai kamar wasu kasashen Turai.”

Ana gudanar da taron ne a daidai lokacin da farashin danyen mai ya kai dala 90 a kowace ganga. Shin wane irin tasiri hakan zai yi a tattalin arzikin duniya. Shugaban babban bankin Jamus Axel Weber ya yi bayani kamar haka.

Weber:

“Idan farashin man ya dore a haka to zai zama babban nauyi akan tattalin arzikin duniya. To sai dai a shekarun baya mun ga yadda tattalin arzikin duniya ya jurewa tashin farashin man, musamman idan farashin ya sake faduwa. Saboda haka wannan ba wani abu ne mai dorewa ba.”

Bisa al´ada a gun taron na bana masu adawa da manufofin jari hujja na gudanar da zanga-zanga a birnin na Washington suna masu zargin asusun IMF da Bankin duniya da yiwa talakawa illa sakamakon sharuddansu na ba da bashi.