1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Somalia a Saudiyya

September 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuB7

Shugabannin kasar Somali dake gudanar da taro birnin Jidda din kasar Saudi Arabia,sun ce suna muradin maye gurbin dakarun kasashen ketare dake marawa gwamnatin rikon baya daga mayakan adawa,da dakarun kasashen Afrika da larabawa,akarkashin kulawar mdd.

A daren jiya ne Shugaba Abdullahi Yusuf,da Prime minista Ali Mohammed Gedi da kakakin majalia Adam Mohammed Nur,sun rattaba hannu a yarjejeniyar amincewa da hakan a gaban Sarki Abdullahi na Saudiyya a Jedda.Cimma wannan matsaya dai yazo ne makonni masu yawa da aka dauka na mahawarar sasanta kasar ta Somalia a birnin Mogadishu.Shugaba Yusuf ya fadawa mahalarta taron Saudiyyan cewa,ayanzu manufarsu itace samar da zaman lafiya,tare da dakatar da zubar da jini.