1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafa wa aikin raya kasa da rashin tsaro a Najeriya

Mohammad Nasiru AwalJuly 17, 2015

Babban taron kasashen duniya kan hanyoyin samar da kudin tallafa wa aikin raya kasashe masu tasowa da rashin tsaro a Najeriya sun dauki hankalin jaridun na Jamus.

https://p.dw.com/p/1G0BC
Äthiopien International Conference on Financing for Development in Addis Abeba
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Wondimu Hailu

To bari mu fara sharhin da birnin Addis Ababa na kasar Habasha inda a wannan makon aka gudanar da taron kolin yini uku kan samar da kudaden tallafa wa aiyukan raya kasashe masu tasowa.

A labarin da ta buga jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta fara da tambayar shin yaya za a yi da batun Afirka? Sannan sai ta ci gaba da cewa.

Hankalin duniya gaba daya ya karkata ga 'yan kasar Girka su miliyan 11, to amma ina batun 'yan Afirka su miliyan dubu daya da dubu dari? A watanni biyar na farko wannan shekara fiye da mutane dubu 100 sun yi kokarin shigowa Turai ta tekun Bahar Rum, don guje wa yake-yake da talauci da rashin aikin yi a kasashen Libya da Siriya da wasu kasashen Afirka. Tun ba yau ba dai shugabannin manyan kasashen duniya ke daukar alkawarin rage matsalar talauci da yunwa amma har yanzu ba a kai gaci ba. Saboda haka ya zama wajibi taron birnin Addis Ababan ya gabatar da sahihan matakai da za su kai ga magance yunwa da talauci a Afirka da kuma sauran kasashe masu tasowa. Ana bukatar jajircewar dukkan sassan da abin ya shafa domin shawo kan wannan matsala.

Tafiya sannu kwana nesa

Shugaba mai go-slow inji jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai cewa ya zame wa sabon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dole ya warware manyan matsaloli da ke gabanshi to amma tun yanzu abin na son ya gagari kundila.

Nigeria Poster von Präsident Mohammadu Buhari vor Militär
Yaki da Boko Haram a Najeriya- sabbin hafsoshin soji, sabon hobasa?Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Ta ce yanzu ne fa shugaban ya cika makonni bakwai da rantsuwar kama aiki amma a dangane da karuwar yawan hare-haren Boko Haram, rashin hankurin 'yan Najeriya na karuwa. Sai dai a wani kokarin na gano bakin zaren matsalar rashin tsaron, a ranar Litinin shugaban ya sallami manyan hafsoshin sojin kasar tare da maye gurbinsu da sababbi. Sai da kawo yanzu hakan bai canja komai a filin daga ba, hasali ma dai aiyukan 'yan bindigar ne ya karu musamman a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da kuma a kasashe makwabta irinsu Chadi da Kamaru da kuma Nijar. Jaridar ta kara da cewa a ranar Lahadi Buhari zai kai ziyara Amirka inda yake fatan samun taimakon gwamnatin Washington a yakin da ake yi 'yan tarzoman a Najeriya.

Gaza daukar matakan magance cin hanci

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon ta leka kasar Yuganda ne da ta kasance 'yar lellen kasashe masu ba da taimakon raya kasa.

Vermittlungsversuch des ugandischen Präsidenten Museveni in Burundi
Shugaba Yoweri Museveni na YugandaHoto: Berthier Mugiraneza/AP Photo

Jaridar ta ce kusan kashi daya cikin uku na kasasfin kudin kasar ta Yuganda na samuwa ne daga kudaden taimakon raya kasa, da yawansu ya kai dala miliyan dubu 1.7. Fannonin kiwon lafiya da ilimi suka fi lakume kudaden tallafin. To sai dai cin hanci da rashawa da wasashen kudin jama'a musamman daga bangaren shugabannin kasar, ya hana wannan tallafin yin wani tasiri na a zo a gani a wadannan fannonin. Maimakon kasar ta yaki cin hanci da rashawa sannan ta dakile hanyoyin wawuran kudaden kasa zuwa aljihun marasa kishin kasa, Shugaba Yoweri Museveni ya mayar da hankali kan man fetir da kasar ta gano a shekarun baya, yana mai cewa wannan arziki zai rage wa kasar dogaro da take kan kudaden taimakon daga kasashen duniya wadanda ke matsa mata lamba kan wasu batutuwa na siyasa.