Taron 'yan tawayen Siriya kan warware rikicin kasar
May 13, 2013Mai magana da yawun 'yan tawayen Siriyan Sonir Ahmed ne ya shaidawa manema labarai hakan inda ya kara da cewa taron na su na kwanaki uku zai gudana ne a birnin Santanbul na kasar Turkiyya in da za su yi kokarin daukar matsayi game da yunkurin sasanta su da gwamantin Assad wadda su ke kokarin hambararwa.
Mr. Ahmed ya kara da cewa za su yi amfani da taron wajen zaben shugabansu bayan da Ahmed Moaz al-Khatib ya yi murabus cikin watan da ya gabata.
A cikin makon da ya gabata ne dai Amurka da Rasha su ka amince da su yi aiki tare kan warware rikicin na Siriya bayan da kasashen biyu su ka jingine banbance-banbancen da ke tsakanin dangane da matsayin da ya kamata a dauka game yakin na Siriya da ya dau kimanin shekaru biyu ana yin sa.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh