Taron Ƙungiyoyin fara hulla a Kenya
January 21, 2007A birnin Nairobi na ƙasar Kenya, ƙungiyoyin fara hulla, sun shiga yini na 2, a taron ƙasa da ƙasa na 7, wanda a karo na farko, ke gudana a nahiyar Afrika.
Dubunan wakilai a wannan gagaramin taro, da su zo daga sasa daban –daban na dunia, za su share kwanaki 5, su na masanyar ra´ayoyi a game da hanyoyin samar da adalci a dunia, tsakanin ƙasashen masu hannu da shuni, da matalauta.
Desmond Tutu, na ƙasar Afrika ta Kudu, wanda ya samu lambar yabo ta zaman lahia, wato Nobel Price, kokuma Prix Nobel, ya bayana mahimnnacin wannan taro:
Abu abu mafi inganci shine, mu jawo hankali masu hannu da shuni kan wasu batutuwa masu mahimmanci: Mu ce da s usu daina shelar cewa babu talauci a dunia su daina iƙirarin cewar akwai adalici a dunia, ta fannin tatalin arziki, sannan su farga da bassusukan da su ka labtawa ƙasashen matalauta zalunci ne.