Tashe tashen hankulan Kenya bayan sakamakon zaɓe
January 1, 2008Talla
Shugaban ƙasar Kenya na cigaba da fuskantar matsin lamba dangane da sakamakon zaɓen kasar ,wanda ya bashi damar zarcewa tare da haifar da rigingimu daya kashe akalla mutane 270 kawo yanzu.Duk dacewar akwai rahotannin cigaban tashe tashen hankula a wasu yankuna dake wajen birnin Nairobi musamman a ɓangaren magoya bayan jamiyyar adawa,kakakin gawamnatin Kenya Alfred Mutua yace lamura sun lafa inda yace gwamnati bata da niyyana kafa dokar hana fita ,ko kuma dokar ta baci,balle amfani da sojoji.A yanzu haka lamura sun fara lafawa ,kuma cikin yan kwanaki kalilan komai zai daidaita dangane da rayuwar jamaa.