1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zambiya ta zama kasar Afirka ta farko da ta gaza biyan bashi

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 8, 2021

Harin da aka kai Jamhuriyar Nijar da tashin hankali a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya gami da cutar coronvirus da ta kassara Afirka ta Kudu na cikin batutuwa da suka dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3ngdA
Niger Symbolbild Terror
Hoto: Boureima Hama/AFP

Bari mu fara da sharhin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta mai taken: sojoji masu yawa, amma babu katabus na azo a gani. Jaridar ta ce 'yan bindiga sun halaka mutane sama da 100 a yankin Tillabéri da ke Jamhuriyar Nijar. Kasar na da karfin sojoji, sai dai yankin ba shi da tsaro, abin da yasa mutane da dama ke neman mafaka daga masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama.

Yayin da yanzu muka shiga sabuwar shekara, a jawabinsa da aka yada a gidajen Radiyo Shugaba Mahamadou Issoufou mai barin gado ya shaidawa al'ummar Nijar cewa: Shekara ta 2020 ta kasance mai tarin kalubale, sai dai wannan sabuwar shekarar za ta zo da kyawawan fata  da za mu cika. Sai dai kwana guda bayan jawabin nasa, sama da mutane 100 sun rigamu gidan gaskiya, sakamkon harin 'yan bindiga a yankin Tillabéri da ke Arewa maso Yammacin kasar. Wannan wani mummunan hari ne a kasar da ta kwashe shekaru tana fama da hare-haren 'yan ta'adda. Koda yake babu wanda ya dauki alhakin wannan hari, sai dai yankin ya saba da fuskantar hare-haren 'yan ta'addan IS da ke Saharar Afirka wato ISGS.

Zentralafrikanische Republik Bangui | vor Wahl | UN-Mission
Hoto: Nacer Talel/Anadolu Agency/picture alliance

Hargitsi ya biyo bayan zabe, in ji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cikin sharhin da ta rubuta tana mai cewa: Tashe-tashen hankula na ci gaba a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Jaridar ta ce: Mako guda bayan zabe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, tashin hankali ya karA kara barkewa a kasar da yaki ya daidaita. Yayin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki da aka gudanar a rabnar 27 ga watan Diusamra bara, an samu tashe-tashen hankula a sasssan kasar da dama in banda Bangui da ke zaman fadar gwamnati, inda aka fafata tsakanin dakarun 'yan tawaye da sojojin gwamnati wadanda ke samun goyon bayan sojojin Rasha da na Ruwanda da kuma Dakarun Wanzar da Zaman Lafiya na Majalisar Dinkin Duniya MINUSCA, wadanda suka kunshi sama da sojoji dubu 12 da suke kasar tun shekara ta 2014.

Tun dai a ranar 31 ga watan Disambar bara, Shugaba Faustin-Archange Touadéra ya gargadi al'ummarsa kan cewa kasar na shirin afkawa cikin yaki. An zargi tsowon shugaba kasar Francois Bozizé da mara wa biyu daga cikin hadakar 'yan tawayen kasar.

Zentralafrika I Wiederwahl von Präsident Faustin Archange Touadéra
Hoto: Nacer Talel/AA/picture alliance

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung, ta rubuta sharnita ne mai taken: Karancin alluran rigakafi, karancin kudi. Jaridar ta ce tilas talakawasu hakura a gama yi wa attajirai. Yayin da ake tsaka da annobar coronavirus karo na biyu, Afirka ta Kudu na nuna tsantsar rashin adalci na duniya wajen yin allurar rigakafin cutar. Sai dai kuma saboda gangami da ake yi, a yanzu mahukuntan kasar sun fara daukar mataki. 

A yanzu lokacin bazara ne a Afirka ta Kudu, sai dai duk da haka a kowace rana yawan wadanda suka kamu da annobar COVID-19 din  na karuwa. Tun a karshen watan Disambar bara, gwamnati ta kara tsaurara dokar kulle, tare da haramta zirga-zirga da kuma shan barasa daga karfe tara na dare, da nufin dakile yaduwar cutar ta coronavirus. An baza sojoji da 'yana sanda domin tabbatar da bin dokar.

Südafrika Corona-Pandemie | Arwyp Medical Centre
Hoto: hafiek Tassiem/REUTERS

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta rubuta mai taken: Afirka na shirin shiga sabon rikicin bashi. Jaridar ta ce Zambiya ce kasar Afirka ta farko a nahiyar Afirka da ta gaza biyan wasu bashin da ake binta sakamakon annobar coronavirus, wasu kasashen za su biyo baya. Cikin watan NUwambar shekarar da ta gabata ne dai, mahukuntan kasar Zambiyan suka fito fili suka bayyana cewa ba za su iya biyan basussukan da wasu kasashen waje ke bin kasar ba. Sai dai wasu kasashen nahiyar ma na cikin tsaka mai wuya na basussukan da ake bin su, kamar yadda wasu hukumomin kasa da kasa kamar Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF da Bankin Duniya suka bayyana.

Matakin na Zambiya dai, na da nasaba da annobar coronavirus da ta kara kassara tattalin arzikin kasar, kasancewar tun ma gabanin annobar Zambiyan na fama da masassarar tattalin arziki.