1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin bama-bamai a Nairobin Kenya

October 13, 2012

An samu tashin bama-bamai a wata unguwa da ta kunshi dimbin 'yan Somaliya a birnin Nairobin kasar Kenya inda 'yan sanda kimanin uku suka jikata. Babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin.

https://p.dw.com/p/16PRw
A fire burns in a clothing stall after an explosion in a shopping complex in Kenya's capital Nairobi, May 28, 2012. A blast struck a shopping complex in Nairobi's business district during Monday's lunch hour, wounding more than a dozen people, but it was not immediately clear what had caused the explosion. Dense black smoke billowed from the badly damaged building and sirens blared as emergency service crews rushed to Moi Avenue, a major road running through the city centre. REUTERS/Johnson Mugo (KENYA - Tags: SOCIETY CIVIL UNREST CRIME LAW)
Hoto: Reuters

'Yan sandan uku sun jikata a Nairobi ne bayan da wasu bama-bamai biyu suka tashi a wata unguwar masu hannu da shuni a babban birnin kasar ta Kenya. Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewar an garzaya da wadanda suka jikata asibiti domin ba su kulawa da ta dace. Har ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin wannan harin. Sai dai an kaddamar da shi ne a kusa da majami'ar da wani yaro ya rasa ransa a watan da ya gabata sakamakon tashin bam.

Hare-hare sun zama ruwan dare a Kenya tun bayan da sojojin kasar suka kutsa Somaliya a shekarar da ta gabata domin yakar masu tsattsauran ra'ayin musulunci na al-Shabab. Dakarun gwamnatin Kenya sun yi nasarar kwato ikon birnin Kismayo a watan da ya gabata sakamakon nasarar fatattakar 'yan al-shabab da suka yi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas