1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin hankalin ƙabilanci a Kenya

Usman ShehuAugust 22, 2012

Wani sabon tashin hankalin ƙabilanci ya hallaka aƙalla mutane 48 a ƙasar Kenya

https://p.dw.com/p/15uFk
An opposition supporter armed with a hammer during protests in the Mathare slum on 16 January 2008. Police fired tear gas and bullets to disperse protesters in several Kenyan cities Wednesday at the start of three days of opposition rallies that threatened to plunge the nation's streets back into post election violence. EPA/BONIFACE MWANGI +++(c) dpa - Report+++
Tashin hankalin da ya faru a kasar Kenya a bayaHoto: picture-alliance/dpa

A kasar Kenya aƙalla mutane 48 suka hallaka a wani fadan ƙarbilanci, tsakanin wasu ƙabilu biyu. Wannan shine tashin hankalin ƙabilanci mafi muni tun bayan tashin hankalin da ya biyo bayan zaben ƙasar shekaru hudu da suka gabata. Babban jami'in yan sanda a yankin Joseph Kitur yace, lamarin ba ken gani, daga cikin wadanda aka hallaka har da mata 31, yara 11, da wasu mazaje 6. Faɗan ta farune tsakanin ƙabilar Pokomo da ta Orma, wadanda ke wani ƙayen a ƙasar ta Kenya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Abdullahi Tanko Bala