1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Radadin corona ya fara lafawa a Jamus

September 1, 2020

Hukumomi a Jamus sun sanar a wannan Talata cewa radadin annobar coronavirus ba zai shafi tattalin arzikin kasar kamar yadda suka yi hasashe tun da farko ba.

https://p.dw.com/p/3hrkE
Angela Merkel lacht
Hoto: Getty Images/AFP/O. Andersen

Hasashen zai ba kasar damar tsara hanyoyin kara samun kudin shiga da kuma duba yiwuwar ko kasar za ta karbi rance a kasafin kudinta na shekara mai zuwa ko kuma a'a. A yayin da yake magana a birnin Berlin Ministan Tattalin Arziki Peter Altmaier ya ce da farko gwamnati ta yi hasashen tattalin arzikin kasar a bana zai samu raguwar kaso 6.3 cikin 100, to amma a yanzu sun fahimci radadin ba zai haura kaso 5.8 cikin 100 ba. 

Ministan ya ce daga abin da suke gani a yanzu za su iya cewa tattalin arzikin Jamus ya fara murmurewa daga radadin coronavirus. Wannan sabon hasashen dai zai ba kasar damar  tsara hanyoyin kara samun kudin shiga da kuma duba yiwuwar ko kasar za ta karbi rance a kasafin kudinta na shekara mai zuwa ko kuma a'a.