Tattaunawa a game da shirin Nukiliyar Koriya ta arewa.
February 12, 2007Talla
Mai yiwuwa a sami ƙarin rana guda a tattaunawar da ake ta ƙasashe shidda a birnin Beijin kan batun nukiliyar koriya ta arewa., abin da ke zama wata alama ta daidaita sabani a tsakanin wakilan wanda aka dora alhakin sa a kan Pyongyang. Tattaunawa ta ci tura a tsakanin ƙasashen shidda a kwanaki huɗun da suka gabata, a game da saɓanin kan wane irin tallafin makamashi ya kamata a baiwa Koriya ta arewan idan ta dakatar da shirin ta na nukiliyar. A cewar jakadan Amurka Christopher Hills, a yanzu dai ya rage ga Koriya ta arewa, yana mai cewa a nasu ɓangaren sun gabatar da shawarwari da zaá cimma masalaha a game da batutuwa da dama.