1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa kan nukiliyar koriya ta Arewa

March 22, 2012

Koriya ta Arewa ta hau kan teburin tattaunawa da hukumar makamashin nukiliya ta duniya wato IAEA da nufin warware rikicin nukilyar ƙasar ta Asiya da ake taƙaddama akai.

https://p.dw.com/p/14PYe
FILE - In this April 5, 2009 image made from KRT video, a rocket is lifted off from its launch pad in Musudan-ri, North Korea. North Korea announced Friday, March 16, 2012, it plans to launch a long-range rocket mounted with a satellite next month, a surprise move that comes weeks after it agreed to nuclear concessions including a moratorium on long-range missile tests. The launch plan comes as North Korea prepares to celebrate the April 15 centenary of the birth of its founder, Kim Il Sung. (Foto:KRT TV, File/AP/dapd) NORTH KOREA OUT, TV OUT
Koriya ta gwada makamai masu cin dogon zango.Hoto: KRT TV

Hukumar makamashin nukiliya ta duniya ta fara tattauna da Koriya ta Arewa da nufin tsayar da ranakun da ƙwararrun masana za su kai ziyarar gane wa idanunsu halin da cibiyoyin nukuliyar ƙasra ke ciki. kakakin gwamnati da ta bayar da wannan sanarwa ba ta bayyana cibiyoyin da jami'an IAEA za su ƙalailaice ba. Wannan matakin na ƙunshe ne cikin yarjejeniyar da Koriya ta Arewan ta cimma da Amirka game da hanyoyin da ya kamata a bi wajen warware taƙadammar nukiliyar ƙasar da ke bin tsarin komunisanci.

Ita dai ƙasar ta Asiya ta amince ta dakatar da gwaje gwajen makamanta masu cin dogon zango, tare da hawa kan teburin shawara da ƙasashen duniya game da wannan batu.Kana Koriya ta Arewan ta amince da tayin da Amirka ta yi mata na tallafa wa al'umarta da ke cikin mawuyacin hali da kayan matsarufi. Rabon jami'an IAEA su kai ziyarar aiki a Koriya ta Arewa, tun bayan da ƙasar ta kori wata tawagar kwararru a shekarar 2009. Tun dai shekaru biyun da suka gabata, ƙasar ta mallaki cibiyar inganta uranium.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal