1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa ta ci tura tsakanin Nijar da ECOWAS

Gazali Abdou Tasawa
January 25, 2024

A Jamhuriyar Nijar ganawar da aka tsara yi da masu shiga tsakani na kungiyar ECOWAS da gwamnatin mulkin sojan Nijar domin share fagen dage wa kasar takunkumin tattalin arziki ya ci tura

https://p.dw.com/p/4bgg9
Still aus DW Webvideo / Lage in Niger nach dem Putsch
Hoto: DW

Bayan kwan gaba-kwan baya zaman da aka tsara za a yi a birnin Yamai tsakanin tawagar masu shiga tsakani na kungiyar ECOWAS da kuma hukumomin mulkin sojan NIjar domin share fagyen tattaunawar da za ta kai ga cire wa Nijar takunkumin kariyar tattalin arzikin da CEDEAO da UEMOA suka saka mata a sakamakon juyin mulki ya ci tura.

Shugabann mulkin sojin Nijar Abdourahamane Tiani
Shugabann mulkin sojin Nijar Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP

Murnar ‘yan Nijar ta koma ciki bayan da tawagar ta ECOWAS da ya kamata ta zo daga birnin Abujan Najeriya ta ci tuwon fashi kamar dai yadda firamnistan kasar Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine ya shaida wa manema labarai.

Dama dai kungiyar Mouvement Patriote da ke goyon bayan sojojin Nijar ta shirya zaman dirshan a babar hanyar filin jirgin saman Yamai domin nuna adawarta da zuwan ECOWAS kamar dai yadda Maicon Zodi shugaban kungiyar ya baiyana

Malam Yahouza Sadissou Madobi, dan siyasa na kasar Nijar
Malam Yahouza Sadissou Madobi, dan siyasa na kasar NijarHoto: DW/A. Mamane

Sai dai Malam Yahouza Sadissou Madobi wani dan siyasa a kasar ta Nijar ya jaddada muhimmancin zaman sulhun a game da wannan matsala ta Nijar.

Ministan harkokin wajen Togo Robert Doussey daya daga cikin masu shiga tsakanin ya iso birnin Yamma, amma zuwan nasa bai yi tasiri ba kasancewar sauran mambobin tawagar basu iso ba. Yanzu dai jama'a sun zura ido su ga yadda kasar Nijar za ta bullo wa ECOWAS domin samun fahimtar juna.