Shirin zaman lafiya a Sudan ta Kudu
May 18, 2018Ana zaman wannan taron mai mahinmancin gaske ga ci gaban Sudan ta Kudu karkashin jagorancin kungiyar AU a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. A yayin da aka koma kan teburin sulhunta dadadden rikici a wannan zama na musanman, shugabanin kasashen yankin da ke makwabtaka da Sudan ta Kudun ba su ce komai kan abin da a ke ganin gazawar shugabanin kasar na shawo kan yakin da ya riga ya lakume rayukan dubban mutane da jefa sauran al'umma cikin halin ha'ula i ba, amman Kwei Quartey mataimakin shugaban hukumar kungiyar ta AU ya baiyana takaicinsa a madadin kungiyar da ya ce za a dauki matakin hukunta masu hannu a zubar da jinin farraren hula.
"Babu tantama na neman ja da matakin kungiyar ta AU kan hukunta wadanda a ka samu ko da laifi ko hannu a kisan 'yan kasa, saboda haka kungiyar ta AU da IGAD da sauran kungiyoyi za su yi aiki tare don ganin an dauki matakin da ya dace kan wadanda suka aikata laifin, shakka babu.''
Wannan ba karon farko ba ne da a ke kokarin shiga tsakani duk da cewa an sha cimma yarjejeniya sai dai kuma bangarorin masu rikici da juna sun karya ka'idojin da aka gindaya, amman yanzu masu shiga tsakani a wannan karon sun mayar da hankali kan wasu muhinman batutuwa a zaman na kwanaki biyar da aka fara daga ranar 17 zuwa 21 ga watan nan na Mayu.
Babbar matsala da kasar ke fuskanta ita ce ta tsaro, inda a ke ci gaba da samun sabanin ra'ayi kan kafa rundunar da dawainiyar tabbatar da zaman lafiya mai dorewa zai rataya wuyanta, duk da haka batu na samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu yana ci gaba da janyo hankulan kasashen duniya da kungiyoyi da ke rajin kare hakkin bil'Adama ya zuwa shugabanin addinai, Archbishop Justine Badi Arama, na cocin Anglican a kasar ya yi tsokaci inda ya ke cewa, lokaci ya yi na ajiye duk sabanin ra'ayin siyasa a yayyafa wa wutar rikicin ruwan sanyi.
Sudan ta Kudu dai na ci gaba da fuskantar matsi musanman daga kasashen Yamma don ganin ta kulla yarjejeniyar samar da zaman lafiya me dorewa.