Tattaunawar ƙawayen Siriya
June 22, 2013Talla
A cikin ministocin har' da John Kerry na Amirka da kuma Laurent Fabius na Faransa, waɗanda suka gargaɗi Iran da ƙungiyar Hizbollah da ta daina ba da agaji na makamai ga gwamnatin Bashar Al-Assad.
Gabanin taron ministan harkokin wajen Birtaniya Williiam Hague da ya ke yin magana da' yan jaridu, ya ce har yanzu ba su bai wa 'yan tawayen na Siriya makamai ba. Kafin wannan taro wani kakakin ƙungiyar 'yan tawaye ya sanar da cewar sun fara samun man'yan makamai daga ƙasashen duniya, waɗanda suka haɗa da masu kakkaɓo jiragen sama na yaƙi da kuma tankokin yaƙi.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman