1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tawagar Ecowas ta gana da sojoji a Mali

Gazali Abdou Tasawa
August 22, 2020

Tawagar jami'an kungiyar Ecowas a karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Googluck Jonathan ta isa a yammacin wannan Asabar a birnin Bamako na kasar Mali da nufin warware rikicin siyasar kasar bayan juyin mulki.

https://p.dw.com/p/3hLhJ
Krise in Mali | ECOWAS | Goodluck Jonathan und Boubou Cissé
Hoto: Présidence du Mali

Tawagar jami'an kungiyar Ecowas a karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Googluck Jonathan ta isa a yammacin wannan Asabar a birnin Bamako na kasar Mali a kokarin da kungiyar take na maido da kasar kan turbar dimukuradiyya bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yi wa gwamnatin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita.

 Kanar Malick Diaw na hannun damar shugaban kwamitin sojojin da suka yi juyin mulkin ne ya tarbo tawagar ta Ecowas a filin jirgi. Da yake jawabi a gaban 'yan Jarida tun a filin Shugaba Jonnathan ya bayyana makasudin zuwan nasu yana mai cewa:O-Ton Jonathan

"Ya ce Ecowas na saka ido kan halin da ake ciki a Mali, shi ya sa muka zo domin tattaunawa da duk bangarorin da ke da ruwa da tsaki a rikicin ta yadda za a cimma wata matsayar da za ta gamsar da al'ummar Mali da Ecowas da ma sauran kasashen duniya"

Bayan ganawa da kwamitin sojojin da suka yi juyin milkin, tawagar ta Ecowas za ta isa a barikin sojoji ta Kati domin ziyartar Shugaba IBK da Firamnistansa Boubou Cisse da shugaban Majalisar dokoki Moussa Timbine da sauran jami'an tsohuwar gwamnatin wadanda sojojin ke tsare da su tun bayan juyin mulkin. A gobe Lahadi tawagar za ta kuma gana da jakadun kasashen Faransa da Amirka rasha Birtaniya da Chaina a kasar Mali.