1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama a tsakanin Koriya ta Arewa da ta Kudu

May 25, 2010

Koriya ta Arewa ta yi barazanar kaiwa Koriya ta Kudu farmaki

https://p.dw.com/p/NWNW
Makamai masu linzami na Koriya ta arewaHoto: DW/AP

Rundunar sojin ƙasar Koriya ta Arewa ta zargi mayaƙan ruwan Koriya ta kudu da yin kutse cikin iyakokin ruwanta, inda ta yi barazanar ɗaukar matakin soji - a matsayin mayar da martani ga abinda ta ƙira shisshigin da Koriya ta kudu ke yi mata.

Wannan zargin da Koriya ta arewa ke yiwa Koriya ta kudun dai, ya zo ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da tada jijiyar wuya a tsakanin ɓangarorin biyu, biyo bayan wani sakamakon binciken daya zargi Koriya ta arewa da alhakin ƙaddamar da wani harin daya yi sanadiyyar la'la'ta babban jirgin ruwar Koriya ta kudu, tare da yin sanadiyyar mutuwar mutane 46 a ranar 20 ga watan Maris na bana.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar Koriya ta arewa ya bayyana cewar, dakarun ƙasar sun miƙa wannan kukan ne ga rundunar koriya ta kudun, game da abin da suka kwatanta da cewar, neman ta'ƙala ce, kuma a shirye rundunar Koriya ta arewa take ta tsunduma cikin yaƙi idan har hakan ya ci gaba.

Wannan cece - kucen dai na zuwa ne bayan da ƙasar Koriya ta kudu ta sanar da cewar, za ta gabatar da kukun ta a gaban kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya da nufin ɗaukan matakin sanyawa Koriya ta arewa ƙarin takunkumi, abinda sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon, ya ce hakanne ya fi dacewa - maimakon kai ruwa rana:

" Na yi kyakkyawan sauraren sanarwar da shugaba Lee na Koriya ta kudu ya yi a daren jiya, inda ya yi ƙira ga Majalisar Ɗinkin Duniya ta shiga tsakani wajen warware batun, ana buƙatar tuntuɓar juna a tsakanin gaggan mambobin kwamitin sulhun. Ina da yaƙinin cewar, kwamitin zai sauke nauyin dake kansa na wanzar da zaman lafiya da tsaro a yankin, ta hanyar ɗaukar matakan da suka dace bisa la'akari da girman matsalar."

Domin neman haɗin kai ɗaukacin wakilan kwamitin sulhun majalisar ne ya sa wani babban jami'in Koriya ta kudu zuwa ƙasar China, wadda ke ƙawance da Koriya ta arewa da nufin neman goyon bayan ta wajen sanyawa Koriya ta arewa ƙarin takunkumi, yayin da a ɗaya hannun, ita ma sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton, wadda ke ziyara a ƙasar China, ta gabatar da makamanciyar buƙatar, kasancewar China ɗin za ta iya hawa kujerar naƙi akan yunƙurin sanyawa Koriya ta arewa ƙarin takunkumin. Sai dai kuma ƙasar China ta yi ta jaddada matsayin ta na cewar, a bi lamarin sannu a hankali domin ɗorewar zaman lafiya a yankin, wanda ta ce dukkan ɓangarori ne za su ci gajiyar sa.

Manazata da dama dai, basa ganin yiwuwar ƙasashen biyu za su faɗa cikin yaƙi duk da wannan taƙaddamar dake tsakanin su da kuma masu kawance tare da su. Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon, ya ce, ci gaba da baiwa Koriya ta arewa tallafin da Koriya ta kudu ta ce za ta yi, abin marhabin lale ne:

" Ina yabawa da sanarwar da gwamnatin shugaba Lee ta bayar, na ci gaba da bayar da agaji na jin kai da kuma tallafawa ƙananan yarar dake cikin ƙuncin rayuwa. A matsayi na na sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, zan ci gaba ta kula da yadda lamura ke tafiya."

A yanzu dai taƙaddama a tsakanin ƙasashen biyu dake zaman doya da manja da juna na ƙara zafafa, wadda kuma ke samun goyon bayan abokan ƙawancen su

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita Yahouza Sadisou