Tilastawa yara aikin soji a Sudan ta Kudu
October 27, 2016Talla
A cewar asusun kula da yara na MDD wato UNICEF lamarin sako wadannan da aka tilastawa shiga yaki, sakin nasu ya faru ne a shekaran jiya Talata. Asusun ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin da ke gaba da juna, da su daina daukan yara kanana ana tilastasu shiga aikin soji. Yaran dai an sako ne daga bangaren mayakan 'yan tawayen SPLA wadanda ke biyayya ga Riek Machar, da kuma wani bangaren mayaka da ake kira Copra, wadanda suka sa hannun zaman lafiya da gwamnati a bariya. An sako yaran ne a jihar Jonglei da ke arewa maso gabashin Juba babban birnin kasar.