1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Timbuktu: Al-Mahdi ya gurfana gaban ICC

Zaharaddeen Lawal / LMJAugust 22, 2016

Shari'ar da ake wa mai rajin jihadin nan dan kasar Mali, Ahmad Al-faqi Al-Mahdi bisa zargin sa da jagoranta rusa wuraren tarirhi a Timbuktu a shekara ta 2012, ta dauki hankali.

https://p.dw.com/p/1JnB4
Ahmad Al-faqi Al-Mahdi na fuskantar shari'a a ICC
Ahmad Al-faqi Al-Mahdi na fuskantar shari'a a ICCHoto: picture-alliance/dpa/P.Post

Wannan shari'a dai ta kasance mai daukar hankali saboda yadda wanda ake zargin ya amsa laifinsa ba tare da bata lokaci ba, abin da ya sanya masu rajin kare ababen tarihi suka yi kiran a yi masa hukunci mai tsanani. A zaman kotun na farko mai gabatar da kara ya yi wa kotu bayanin cewa Ahmad Al-faqi Al-Mahdi mamba ne a kungiyar 'yan ta'addan Ansar Dine wadda ke da alaka da kungiyar Al-qaida, ana kumazargin sa ne da jagorantar ayyukan rushe guraren tarihi a Mali a shekara ta 2012, ya kuma shiga hannu ne bayan da dakarun sojojin Faransa suka cafke shi a shekara ta 2014.

'Yan ta'adda na rusa guraraen tarihi a Tinbuktu
'Yan ta'adda na rusa guraraen tarihi a TinbuktuHoto: Getty Images/AFP

Bayan an karantawa Al-Mahdi laifukansa, sai mai shari'a ya tambaye shi ko ya gane abin da ake tuhumar sa, inda shi kuma ya kada baki ya ce ya gane, tare kuma da amsa laifinsa yana mai cewa:

Amsa laifi da nadama

"Ya ku maza da mata da ke wannan kotu, ina mai matukar nadama da nuna bakin ciki a yau, dukkan laifukan da aka zayyana a kaina tabbas haka suke, ina mai neman afuwa bisa abin da na aikata ga al'ummar Timbuktu da iyalaina da kuma kasata ta Mali, na yi takaicin wannan rushe-rushen."

Al-Mahdi shi ne mai fafutukar jihadi na farko da yake fuskantar tuhuma a gaban kotun hukunta masu aikata manyan laifukan yaki ta kasa da kasa wato ICC da ke da matsuguni a birnin The Hague na kasar Netherlands, kuma mutum na farko da ya amsa laifinsa a gaban wannan kotu tare da bayyana cewa ya yi matukar nadamar umartar rusa wuraren tarihin a Tumbuktu, inda kuma ya yi fatan babu wani Musulmi a duniya da zai yi koyi da abin da ya aikata a nan gaba.

Mahukunta da mazauna birnin Timbuktun dai, sun ce sun yi farin ciki saboda mutumin da ya jagoranci rusa guraren tarihi na fuskantar shari'a, Halle Ousmane shi ne magajin garin Timbuktu, ga kuma abin da yake cewa:

Ahmad Al-faqi Al-Mahdi a gaban kotun ICC
Ahmad Al-faqi Al-Mahdi a gaban kotun ICCHoto: picture-alliance/dpa/P.Post

"An tabbatar da shari'ar da ta can-canta, muna godiya ga Allah, mun kuma godewa dukkan wadanda suka taimaka wajen gurfanar da Ahmad Al-mahdi a gaban shari'a, babu wadda yafi karfin shari'a."

Nasarar farko ga kotun ICC

Amsa laifin da Al-Mahdi ya yi dai a gaban kotun ta ICC, wata babbar nasara ce ga kotun a karon farko tun bayan da aka kafata a 2002 da zummar hukunta masu aikata manyan laifukan yaki, to sai dai wasu da dama na kallon wanann kotun da cewa tafi gurfanar da bakaken fatar Afirka, zargin da kotun ta ICC ta sha musantawa. Kotun dai za ta yanke hukunci a zamanta na gaba, Ahmad Al-faqi al-mahdi zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 30, to sai dai masu gabatar da kara zasu nemi a daure shi shekaru tara ko 11.