1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen kafa sabuwar gwamnati

Ubale Musa SB/ZMA
March 17, 2023

A ci gaba da shirye-shiryen kamun iko, sabon shugaban Najeriya da ke shirin hawa gado ya yi watsi da batun gwamnatin hadin kai na kasa da masu adawa ke neman gani cikin kasar bayan zabe mai zafi.

https://p.dw.com/p/4OpzD
Bola Tinubu I Najeriya
Bola Tinubu zababben shugaban Najeriya Hoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

Ya zuwa yanzu dai ana kara dagun hakarkari bisa sakamakon da ya kai ya zuwa bullar Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin sabon shugaba na Najeriya. Abun kuma da ya kai ga masu siyasa ta kasar tunanin hada kai da nufin kaucewa barazanar raba kai da kila ma siyasar gaba cikin kasar.

Karin Bayani: Najeriya: 'Yan adawa sun ki aminta da zabe

To sai dai kuma sabo na shugaban kasar ya ce ba shi tunanin hada kan da adawa a cikin dabarun mulki. A cikin wata sanarwar da ya kai ga fitarwa dai Tinubu ya ce hankalinsa zaifi karkata ya zuwa cancanta ne da nufin neman mafita cikin kasar dake da tarin rudani. Kalaman kuma da daga  alamu ke iya kara jawo rabuwa a tsakanin masu siyasar cikin kasar a halin a yanzu.

Najeriya Zaben shekara ta 2023
Zaben Najeriya na shekara ta 2023Hoto: Abraham Achirga/REUTERS

A shekara ta 2007 dai alal ga misali batun hadin kan ne ya kai ga ceto kasar bayan wani zaben da shi kansa wanda ya yi nasara ya ce yana da sauran gyara.

To sai dai kuma in har masu tsintsiyar suna shirin fifitar cancantar daga dukka na alamu suna da jan aikin lalalshi haar a cikin jam'iyyun na adawa. Shehu Musa Gabam dai na zaman shugaban jaam'iyyar SDP na kasa daya kuma a cikin jam'iyyu 18 da suka taka rawa a zaben na shugaban kasar da ya shude.

Koma ya take shirin da ta kaya a tsakanin masu tunanin suna da farcen susa da kuma 'yan kallon tuwa namu man shanun namu, batun cancantar na zaman wajibi a cikin neman shawo kan jerin rigingimun da ke kasa a fadar Mohammed idris Malagwi da ke zaman daya a cikin daraktocin yakin neman zaben Bpla Tinubu.