Tony Blair ya kare shigar Britaniya a yakin Iraq da Afghanistan
January 12, 2007Firaministan Birtaniya Tony Blair ya kare katsalandar da sojojin kasar sa suka yi a Afghanistan da Iraqi, yana mai cewa matakan diplomasiya kadai ba zasu warware matsalolin da duniya ke fuskanta ba. A wani jawabi da ya yiwa sojojin kasar a birnin Plymouth mai tashar jiragen ruwa, Blair ya ce dole a hada matakan diplomasiya da wasu matakai masu tsauri kamar na soji don yakar ayyukan ta´addanci. To sai dai duk da haka Blair ya amsa cewar matakan sojin da Birtaniya ta dauka a kasashen Afghanistan da Iraqi yana barazanar gagarar karfin rundunar sojin ta. Ya ce dole ne a kara kasafin kudin rundunar sojin muddin a na son a ci-gaba da aiwatar da manufar sa ta soji. Jawabin na sa ya zo ne kwana guda bayan sanarwar da Amirka ta bayar ta tura karin sojoji kimanin dubu biyu a Iraqi.