Trump da Kim - dandali ga masu zanen barkwanci
Shugaban Amira Donald Trump da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un na sanya fargaba a zukatan al'umma a dangane da barazanar makaman nukiliya. Amma takaddamarsu ta bude sabuwar kafa ta barkwanci.
Kokuwar askin baba
Ana bukatar rokoki biyu masu suma, daya mai launin gwal, an matso da ita gaba, dayar kuma baka an daga ta tamkar buroshi. Kuma kowa na iya ganewa nan-take wanda ake nufi.
Askin baba na masu takadammar nukiliya
Trump: "Askina ya fi burgewa!" Kim: "Amma nawa gagarabadau ne!!"
Fito na fito na marasa hangen nesa ...
Sun tambayi juna: "Shin kai ba ka da tunani ne?"
Ba abin da ya kai tusa
Bisa ga dukkan alamu matasan nan biyu sun sauya tusarsu ta nukiliya ya zuwa wani yanayi na kan wata.
Tantabaru da makaman nukiliya
Sakonnin Twitter na Shugaba Trump sun rikide sun zama makaman nukiliya sun doshi Koriya ta Arewa.
Hotuna 5
1 | 5Hotuna 5