1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump da Kim sun kafa tarihi a Singapour

Gazali Abdou Tasawa
June 12, 2018

Shugaba Donald Trump na Amirka da takwaransa Kim Jong Un na Koriya ta Arewa sun yi ganawa mai cike da tarihi da ke zama ta farko tsakanin wani shugabanni da ke kan mulki a kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/2zKXp
Singapur Gipfel Kim Jong Un Donald Trump
Hoto: Reuters/A. Wallace

Shugabannin biyu sun yi musabaha da juna a wannan Talata a cikin wani yanayi mai cike da tarihi da ke zama musabaha ta farko da aka yi tsakanin wani shugaban Amirka da ke kan mulki da kuma wani shugaban Koriya ta Arewa.

 A lokacin wannan haduwa wacce ta gudana a wani kasaitaccen Hotel na tsibirin Senatosa a Singapour Shugabannin biyu sun yi doguwar musabiha cikin murmushi a gaban jerin tutocin kasashen nasu guda biyu. 

Shugabannin biyu sun yi ganawar keke da keke ta kimanin mintoci 50. Kuma da yake jawabia gaban 'yan jarida a karshen wanann ganawa Shugaba Trump ya ce ganawar ta yi armashi sosai fiye da duk yadda wani mutun zai iya tsammahani. Shima dai Shugaba Kim Jong Un ya bayyana farin cikinsa da saduwa da Shugaba Trump inda ya ce lalle sun sha daga kafin su kai ga cimma wannan nasara. 


Shugabannin biyu dai sun saka hannu kan wasu takardu inda Shugaba Donald Trump ya sha alwashin tabbatar da tsaron lafiyar Koriya ta Arewa. Kazalika Shugaba Trump ya bayyana cewa za su ci gaba da ganawa lokaci-zuwa lokaci da takwaran nasa Kim jong Un wanda ya ce zai gayyata a fadarsa ba da jimawa ba.