Trump da Kim sun rattaba hannu kan kudiri
June 12, 2018Shugaban Amirka Donald Trump na kan hanyar komawa gida bayan ganawa mai cike da tarihi da ta gudana tsakaninsa da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un a taron kolin da suka kammala yau Talata a kasar Singapore.
Shugabannin biyu sun rattaba hannu akan daftari na bai daya wanda ya jaddada kudirin Pyongyang na kawar da makaman nukiliya daga yankin tsibirin Koriya.
Da yake jawabi ga manema labarai shugaban Amirka Donald Trump yace yana fata nan ba da jimawa ba za a fara aiwatar da shirin kawar da makaman nukiliyar daga yankin Koriya.
"Yace ni da Chairman Kim mun sanya hannu akan wasu bayanai na bai daya inda ya jaddada kudirinsa ga kakkabe makaman nukiliya daga yankin tsibirin Koriya."
Bugu da kari kudirin ya tanadi cewa Amirka za ta bada tsaro wanda ba'a fayyace shi ba ga Koriya ta Arewa. Hakannan sun yi alkawarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tsibirin Koriya baki daya.
Wannan dai shine karon farko da wani shugaba na Amirka da ke kan mulki ya gana da wani shugaban kasar Koriya ta Arewa.