Trump a sahun masu tuna da ranar D-Day
June 6, 2019Talla
Bbikin da ake wa lakabi da D-Day na wannan lokaacin dai shi ne karo na 75, kuma an gudanar da shi cikin yanayi na harba bindigogi a sama da faretin girmamawa. Shugaba Donal Trump na Amirka da Emmanuel Macron na kasar Faransa sun yi tsit a wurin bikin tunawa da sojojin da suka mutu lokacin yakin duniya na biyu. Sama da mutane 60 daga kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya da suka tsira bayan yakin mamaya a watan Yuni na shekara ta 1944 da har yanzu suke raye sun halarci bikin na bana.