Trump da Macron sun tattauna abubuwa da dama
April 24, 2018Shugaban kasar Faransa da mai masaukin bakinsa a birnin Washington Donald Trump, sun tattauna a ofishin shugaban inda suka tabo batutuwa da dama kama daga batun sojan Amirka a Siriya da Trump ya ce za su bar kasar ba da dadewa ba, shi kuwa Macron ya ce hanyar diflomasiya za a bi wajen warware rikicin na Siriya idan an gama kawar da kungiyar IS, abin kuma zai dau lokaci, sai batun dangantaka da Koriya ta Arewa da Trump ya ce alamu na nuni da cewa Shugaban Koriya ta Arewa na magana ba boye-boye da batun Iran da Trump ya ce batun ta koma kan shirin makamashin nukiliya na da hadari wanda ya ce za su yi aiki da Faransa kan wannan batu.
Haka nan shugabannin sun tabo baban batu na kasuwanci tsakanin Amirka da Turai inda Trump ya ce kasuwanci da a ce da Faransa ita kadai ce da mai sauki ne amma batu ne na kasuwanci da kasashen na EU baki daya wanda ba mai sauki ba ne saboda sharuda.