Dubban Amirkawa na fuskantar hadarin corona
April 1, 2020Shugaban Amirka Donald Trump ya shaidawa Amirkawa cewa su kasance cikin shiri domin jure wa matsanancin hali da za a shiga cikin 'yan makonni masu zuwa.
Fadar gwamnatin ta Amirka ta bukaci Amirkawa su shirya tunkarar karuwar mace macen jama'a tsakanin 100,000 zuwa 240,000 cikin 'yan watanni masu zuwa.
Sai dai jami'an lafiya sun ce ana iya kaucewa wannan hali idan jama'a a fadin kasar suka cigaba da kasancewa nesa da juna.
A halin da ake ciki dai mutane fiye da 4,000 suka mutu a Amirka sakamakon cutar coronavirus yayin da adadin wadanda suka kamu ya haura 170,000
A waje guda kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ja hankali da cewa halin da al'umma suka shiga a yanzu shine mafi muni tun bayan yakin duniya na biyu.
Kusan rabin al'ummar duniya na cikin yanayi na killacewa yayin da gwamnatoci ke kokarin dakile yaduwar cutar da a yanzu ta harbi mutane fiye da 840,000 a duniya yayin da mutane 40,000 kuma suka rasu yawancinsu a kasashen Spain da Italiya.
A Jamus hugabar gwamnati Angela Merkel za ta gana da Frimiyan jihohi a fadin kasar a wannan larabar domin tattauna karin matakai na shawo kan cutar.
Gwamnatin ta kafa dokar takaita zirga zirga da haramta tarukan jama'a fiye da mutum biyu.