1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan takarar Republican ya yi zargin magudi

Lateefa Mustapha Ja'afarFebruary 3, 2016

Dan takarar shugabancin kasa a Amirka karkashin inuwar jam'iyyar Republican da ya sha kaye a zaben fidda gwani na jihar Iowa Donald Trump ya yi kira da a sake zaben da aka yi a jihar.

https://p.dw.com/p/1HpRn
Dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar Republican ta Amirka Donald Trump
Dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar Republican ta Amirka Donald TrumpHoto: Reuters/J. Bourg

Trump dai ya zargi abokin hamayyarsa Sanata Ted Cruz da ya lallasa shi a zaben da yin magudi, inda ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa:"Ted Cruz bai lashe zaben Iowa ba, ya sata ne. Shi ya sa baki dayan kuri'un akwai kuskure, kuma ya samu kuri'u fiye da tsammani. Abin takaici."

Hamshakin dan kasuwar Donald Trump ya sha kaye a hannun abokin hamayyarsa Ted Cruz inda ya zo na biyu a yayin zaben fidda gwanin da aka gudanar a jihar Iowa a ranar Litinin din da ta gabata, wanda kuma dama shi ne zakaran gwajin dafi na wanda ka iya lashe zaben shugaban kasar ta Amirka.