1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya ce babu tabbas ya amince da sakamakon zabe

October 20, 2016

Donald Trump, ya ce shi dai ba zai iya daukar wani alkawari ba kan cewa zai  amince da sakamakon zaben shugaban kasar Amirka da za a gudanar a watan Nowamba.

https://p.dw.com/p/2RSZY
USA | Ende der 3. Präsidentschaftsdebatte 2016 in Las Vegas
Hoto: REUTERS/M. Blake

A kasar Amirka a wani abin da ke zama sabo ga al'adar jam'iyyar Republicain, dan takarar neman shugabancin Amirka a karkashin inwar jam'iyyar wato Donald Trump, ya ce shi dai ba zai iya daukar wani alkawari ba kan cewa zai  amince da sakamakon zaben shugaban kasa da kasar za ta shirya a farkon watan Nowamba mai zuwa.

Ya bayyana hakan ne a lokacin muhawarar kai tsaye ta talabijin da ya fafata a daren jiya da abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton inda da dan jaridar da ke jagorancin muhawarar ya tambaye shi ko zai amince da sakamakon zaben sai ya amsa yana mai cewa:

Ya ce: "Zan duba in gani a lokacin, domin abin da na gani ba mai kyau ba ne, dan wasu daga cikin kafofin yada labaran munafukai ne kuma shafaffu ne da mai. Dan haka ba zan bayar da wannan amsa ba a yanzu, na bar ku  ku yi tunani"

Hillary Clinton dai ta bayyana wadannan kalamai na Donald trump a matsayin na kaskantar da demokradiyya da cin mutuncinta. A duk tsawon lokacin muhawarar dai kowanne daga cikin 'yan takarar biyu ya yi ta zargin dan uwansa inda Hillary Clinton ta zargi Donald Trump da kasncewa dan kazagin Shugaba Poutine na Rasha a yayin da shi kuma Trump ya zargi Hillary Clinton din da kasancewa ummulhaba'isan zargin cin mutuncin mata da wasu jerin mata suka yi masa a baya bayan nan.