1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya jaddada aniya kan Koriya ta Arewa

Gazali Abdou Tasawa
April 11, 2017

Shugaban Amirka Donald ya jaddada a wannan Talata aniyarsa ta yin gaban kansa wajen shawo kan rikicin nukiliyar Koriya ta Arewa ba tare da neman taimakon kasar Chaina ba.

https://p.dw.com/p/2b3fg
USA Trump - Giftgasangriff in Syrien
Hoto: Reuters/Y. Gripas

Shugaban Amirka Donald ya jaddada a wannan Talata aniyarsa ta yin gaban kansa wajen shawo kan rikicin nukiliyar Koriya ta Arewa ba tare da neman taimakon kasar Chaina ba. Shugaba Trump ya bayyana haka ne a shafinsa na Tweeter inda ya ce Koriya ta Arewa na neman tashin hankali ne. 

Idan har Chaina za ta iya maido ta kan turba to hakan zai fi zama alkhairi. Amma a shirye Amirka take ta dauki matakin da ya dace. Wadannan kalamai na shugaba Trump sun zo ne kwanaki kalilan bayan ganawasa da takwaransa na Chaina Xi-Jinping. 

Yanzu haka dai Koriya ta Arewar ta harzuka a game da matakin da Amirkar ta dauka na tura kayan yaki da sojoji a yankin tekun Pacific na kasar ta koriya ta Arewa.