1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump: Ya kare antoni janar na kasar Amirka

Yusuf Bala Nayaya
March 3, 2017

'Yan Democrats na cewa antoni janar din na Amirka ya sauka daga mukaminsa saboda ba daidai ba yayin da Trump ke cewa mutum ne mai gaskiya.

https://p.dw.com/p/2YZgZ
Jeff Sessions
Hoto: picture alliance/dpa/Sipa USA

Shugaba Donald Trump na Amirka ya yaba wa antoni janar na kasar Jeff Sessions inda ya zargi 'yan jam'iyyar Democrats da yi masa bita da kulli irin na siyasa kan batun alakarsa da jakadan kasar Rasha gabannin su hau karagar mulkin Amirka ko ma lokacin da su ke yakin neman zabe.

Sessions dai a ranar Alhamis ya zame kansa cikin tawagar binciken katsalandan na Rasha a zaben na Amirka a shekarar bara. An dai yi zargin cewa yaki bada amsa har sau biyu bayan da aka tambaye shi kan alakarsa da jakadan Rasha a lokacin da ake tantance shi kan wanna mukami.

A daren na jiya Alhamis dai Shugaba Trump ya bayyana Sessions a matsayin mai gaskiya kuma 'yan Democrats na shure-shure ne wanda ba ya hana mutuwa ne.