Trump ya sa baki a rikicin yankin Gulf
July 14, 2017Talla
Fadar White House ta sanar da tattaunawar da shugaba Donald Trump ya yi da sarki Salman na Saudiyya, inda sanarwar ta yi karin bayani kan batun warware rikicin kasar Katar da wasu kasashen yankin Gulf hudu, kan zargin da ake yi wa Katar na tallafawa harkokin ta'addanci. An dai yi tattaunawar ce ta wayar tarho wanda ke zuwa bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurkan Rex Tillerson ya kai yankunan na Larabawa.
Kasashen Larabawa sun zabi yanke hulda da kasar Katar bisa zarginta da tallafawa kungiyoyi na masu tada kayar baya, zargin da Katar ta musanta.