1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Trump ya sake tsallake rijiya da baya a yunkurin halaka shi

September 16, 2024

Tsohon shugaban na Amurka ya na filin wasansa na golf, a yayin da maharin dauke da bindigar AK-47 ya nemi yin harbi.

https://p.dw.com/p/4keew
Donald J. Trump
Donald J. Trump Hoto: Kyle Mazza/NurPhoto/picture alliance

Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump ya sake tsallake rijiya da baya a wani sabon hari da wani dan bindiga ya yi yunkurin kai masa a filin wasansa na kwallon lambu a birnin Florida.

To sai dai kuma babu abinda ya samu Trump a wannan karon bayan jami'an hukumar FBI sun bayyana cewa sun dakile yunkurin kisan nasa.

Shugabannin duniya sun yi tir da harin da aka kai wa Trump

Da yawa daga cikin jami'an sun yi ta harbi cikin daji ta inda aka ji motsi bayan ganin mutumin a dan tazara tsakaninsa da inda Trump ke wasa a cewar hukumomi.

Mutumin da ake zargi ya bar bindiga kirar AK-47 da kuma wasu kayayyaki bayan ya ranta a na kare cikin wata mota, sai dai daga bisani an cafke shi.

Wannan yunkurin kisan Trump na zuwa ne watanni biyu bayan an yi masa rauni a kunnen dama da bindiga yayin yakin neman zabe a Pennsylvania.

Harris ta sa Trump kare kansa a zazzafar muhawara

Wadannan lamuran da suka faru na nuna kalubalen da ke gaban jami'an tsaro na tabbatar da tsare rayukan 'yan takara a zaben Amurka dake tafe cikin watan Nuwamban shekarar 2023.