1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya sauya matsayarsa kan Afganistan

Yusuf Bala Nayaya
August 22, 2017

A jawabin da ya gabatar a daren Litinin Shugaba Trump ya bayyana cewa sojan na Amirka za su kara damara har sai sun ga bayan mayakan Taliban.

https://p.dw.com/p/2icHk
USA Fort Myer Trump Rede Afghanistan Strategie
Hoto: Getty Images/M. Wilson

A wani mataki da ke nuna yin kwana kan alkawuransa a lokacin yakin neman zabe, Shugaba Donald Trump a daren ranar Litinin ya bayyana cewa Amirka za ta ci gaba da kokari na ganin ta kakkabe burbushin rikici a kasar Afganistan, bayan nuna cewa kasar za ta iya kara tura dakaru zuwa kasar a fadan da take yi da ba za ta saurara ba har sai ta yi nasara.

A jawabin da ya gabatar a daren Litinin Shugaba Trump ya bayyana cewa sojan na Amirka za su kara damara har sai sun ga bayan mayakan Taliban a kasar:

Trump dai ya ce yadda ya kalli batun tura dakarun kafin hawansa mulki ya sha bambam da abin da ke a zahiri. Wasu jami'an gwamnatin kasar ta Amirka dai sun bayyana cewa kasar za ta kara tura dakaru 4000, abin da zai sa adadinsu ya kai 8,400.

Taliban dai ta mayar da martani inda ta ce wannan mataki na Trump kara samar da kaburbura ne na sojan Amirka da za su halaka a Afganistan.