Trump ya soke dokar kasuwancin TPP
January 23, 2017Ranar aiki ta farko bayan ranzuwarsa, Shugaban kasar ta Amirka Donald Trump, ya fara aiwatar da mahimman alkawura da ya yi a lokutan yakin neman zabe. Inda ya sa hannu kan wasu ayoyin doka. Daga cikin dokar da aka soke, har da kasuwancin bai daya, wanda aka cimma a tsakanin Amirka da wasu kawayenta, yarjejeniyar wace aka sani da TPP, kana ya sa hannu domin soke kudin gwamnatin Amirka ke baiwa kungiyoyi masu zaman kansu, wadanda ke bada tallafi a kasashen waje ga ayyukan zubar da ciki. Sabon shugaba Trump, ya kuma bada goron gayyata ga Firimiyar Birtaniya Threasa May, wace za ta kawo ziyara a ranar Juma'a mai zuwa. Wannan dai ita ce ranar farko ta aiki, bayan ranzuwar Trump a matsayin shugaban kasa. Sa hannun kan wadannan ayoyi da ya soke su a yau Litinin, ya kara tabbatar cewa sabon shugaban na Amirka, da gaske yake kan batutuwan da ya fada lokacin yakin neman zabe.