1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya yi barazana kan gina katanga

Yusuf Bala Nayaya MNA
January 9, 2019

Shugaba Donald Trump na Amirka ya yi kira tare da jan hankali ga al'ummar kasar Amirka a kokari na jan hankalinsu ga irin barazanar tsaro da da tashin hankali daga yankin iyakar kasar da Mexiko.

https://p.dw.com/p/3BDlK
Präsident Trump spricht vom Oval Office aus die Nation zur Grenzsicherheit an
Hoto: Getty Images/C. Barria-Pool

A wata murya da bakasafai yake yin ta ba Trump ya nuna yadda matsaloli hadi da na tsaro ke karuwa a iyakar Amirka da Mexiko inda ya ce batun samar da katanga a iyakar abu ne mai muhimmanci ga tsaron kasar. Domin ganin ya ja hankali, shugaban na Amirka ya rika ba da misalai na wasu abubuwa na tashin hankali da ake gani a kan iyakar.

Da yake kara jaddada bukatarsa ta ganin 'yan majalisa sun amince masa da kashe Dala miliyan dubu biyar da dari bakwai don gina katangar ya nemi 'yan jam'iyyar Democrats su dawo su gana da shi a fadar White House. Ya ce kin yin wani abu a bangaren 'yan majalisar abu ne da ya sabawa yin da'a.