Trump ya yi barazanar ragargaza Pyongyang
September 20, 2017Shugaba Donald Trump na Amirka ya yi gargadi a ranar Talatar nan cewa za a tilasta wa Amirka ta dauki mataki na "ragargaza" Koriya ta Arewa muddin mahukuntan birnin na Pyongyang ba su tsayar da shirinsu na hada makamin nukiliya ba. Ya kwatanta Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa a matsayin mutum da ke cikin makamin roka da ya dauki aniya da kama hanya ta aiwatar da kisan kansa da gwamnatinsa. Trump ya nemi kasashen duniya da su mayar da Koriya ta Arewa saniyar ware har sai ta sauya aniyarta ta mallakar makamin nukiliya. Har ila yau Trump ya kuma tabo batun kasar Banizuwela inda ya ce halin da mahukuntan Banizuwela masu ra'ayin gurguzu suka sa kasar ba abu ne da za a lamunta ba, "dole 'yanci na demokaradiyya da walwala ya samu gindin zama."
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na daga cikin shugabannin duniya da a wannan Talata suka yi jawabi a gaban babban taron na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya tabo rikicin kasar Myanmar yana mai kwatanta halin da Musulmi 'yan kabilar Rohingyas ke ciki da kisan kare dangi da ya auku a Bosniya a shekarar 1995 da kuma Ruwanda a shekarar 1994. Ya bukaci shugabannin duniya da su yi tir da abin da ya kira kisan tsabtace kabila a Myanmar. Ya kuma gode wa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da rage wahalhalun da 'yan gudun hijira ke fuskanta.