Trump ya yi jinjina ga Kim Jong Un
April 24, 2018Talla
Shugaba Donald Trump na Amirka ya yi yabo da jinjina ga Shugaba Kim Jong Un inda ya ce "mutum ne da ba shi da boye-boye" me kuma "cikar kima", ya kara da cewa shugaban na Koriya ta Arewa na son su gana nan ba da dadewa ba. Ya ce suna tattaunawa me cike da fahimta tsakaninsu. Shugaba Trump ya bayyana haka ne gabannin tattaunawar da za su yi da shugaba Kim Jong Un wacce ake sa rai a yi kafin karshen watan Yuni. Trump ya ce mutum ne wanda ba ya boye komai da ke zuciyarsa, yana ganin "ya cancanci mutuntawa matuka."