1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya yi watsi da tayin soke izinin mallakar bindiga

Gazali Abdou Tasawa
March 28, 2018

Shugaba Donald Trump na Amirka ya yi watsi da kiran da wani babban alkalin kasar ya yi masa na yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin soke kudirin da ya halasta wa Amirkawa izinin mallakar bindiga. 

https://p.dw.com/p/2v8hB
Deutschland - sichergestellte Waffen - ZIT in Gießen
Hoto: picture alliance/dpa/A. Dedert

A cikin wani sako da ya wallafa a wannan laraba a shafinsa na Tweeter, Shugaba Trump ya bayyana cewa har abada ba za a soke wannan kudiri ba. A jiya Talata ce alkali John Paul Stevens tsohon mamba a kotun kolin kasar ta Amirka ya yi kira ga Shugaba Trump da ya soke kudirin da ya bai wa Amirkawa izinin mallakar bindiga wanda karni biyu kenan ake cece-kuce da ma sabanin fahimta kansa. 

Masu fafutukar kare 'yancin mallakar bindiga a kasar ta Amirka dai na kallon wannan kudiri na izinin mallakar bindigar a matsayin wani abu mai matukar muhimmanci ga rayuwar Amirkawa.