1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya zargi tsohon lauyansa Cohen

Salissou Boukari
August 23, 2018

Shugaban Amirka Donald Trump ya mayar da martani a shafinsa na Twitter dangane da shari'ar da ake yi wa Paul Manafort tsohon jagoran tawagar yakin neman zabensa, da kuma tsohon lauyansa Michael Cohen.

https://p.dw.com/p/33efc
Kombi-Bild - USA Russland-Affäre - Donald Trump, Michael Cohen und Stormy Daniels
Shugaban Amirka Donald Trump, da tsohon lawyansa Michael Cohen, da kuma Stormy DanielsHoto: picture alliance/AP

A shafin nasa na Twitter, Trump ya bai wa Paul Manafort tsohon jagoran yakin neman zabensa hakuri. Shi dai Manafort ana zarginsa da aikata manyan laifuka har 18, ciki kuwa har da kin biyan kudaden haraji na tsawon shekaru 12. Trump ya rubata a shafin nasa cewa yana girmama Manafort a matsayin jajirtaccen mutum, wanda ya jurewa duk wani matsin lamba. Sai dai Trump ya bayyana tsohon lauyansa Michael Cohen a matsayin makaryaci wanda ya kware a iya kirkirar labari mara tushe. A hannu guda lauyan da ke kare Cohen ya ce amincewa da Cohen ya yi da laifinsa babban hadari ne ga Trump. Lauyan na Cohen mai suna Lanny Davis ya kara da cewa:

Michael Cohen
Tsohon Lawyan Trump Michael Cohen da jami'an tsaroHoto: picture-alliance/AP/M. Altaffer

"Abin da na lura da shi, shi ne Mr. Cohen ya san wani abu da mai binciken na musamman ke bukata, misali ko Donald Trump ya san cewa za a yi kutse a wasikun na Email wanda aka tuhumi wasu 'yan kasar Rasha su 12 a kai. Tilas mu jira mu ga abin da Cohen zai iya cewa in har ya yi magana da mai binicken na musamman."

Tuhumar da ake wa Paul Manafort ce ta farko, kamar yadda mai bincike na musamman Mueller ya tsara. Manafort ya jima a matsayin jagoran yakin neman zaben Trump. Tilas ya amsa wasu laifuka da ya tafka a baya, ciki kuwa har da kaucewa biyan haraji da kuma amfani da wasu asusun ajiya ta hanyar da ta saba ka'ida. A shafinsa na Twitter, Trump ya nuna tausayawa ga Manafort. A hirarsa da gidan talabijin na CNN Sanata Richard Blumenthal daga jam'iyyar Democrats ta adawa, ya nunar da cewa Trump na son a yafewa Manafort laifinsa ne:

USA - Ermittlungen zur Russland-Affäre - Trumps Ex-Anwalt Michael Cohen
Hoto da ke nuni da yadda Michael Cohen ya bayyana a gaban alkaliHoto: Reuters/J. Rosenberg

"Muna cikin wani rikici da yai kama da na shekarun 1970 da ya yi awon gaba da gwamnatin Shugaba Richard Nixon. Tilas jam'iyyun biyu su yi aiki tare. Ya zama wajibi mu kare mai binciken na musamman, mu kuma dakile duk wani mataki na yadda da yafiya. Shugaban kasa zai iya yafewa Manafort amma hakan zai nunawa duniya cewa ya aikata laifin da ake zarginsa. Zai rage darajar ofishinsa. Tashin hankali."

Trump da kansa da kuma magoya bayansa na kokarin ganin sun fitar da sunansa daga cikin tuhumar da ake wa Manafort suna masu cewa ya aikata laifukan da ake zarginsa ne kafin ya fara aiki da Trump.