Trump zai gana da shugaban Falasdinawa
April 19, 2017Talla
Shugaba Donald Trump na Amirka zai karbi bakunci na Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ranar uku ga watan Mayu kamar yadda fadar White House ta bayyana a ranar Laraban nan.
Da ya ke ganawa da manema magana da yawun fadar ta White House Sean Spicer ya ce wannan dama ce da Shugaba Donald Trump da Mahmoud Abbas za su yi amfani da ita wajen lalubar hanyoyi da za su kai ga warware matsalar da ta ki ci taki cinyewa tsakanin Falasdinawa da 'yan Isra'ila.