1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsagerun Niger Delta sun sake yin garkuwa da wani mutumin

August 16, 2006
https://p.dw.com/p/BumU

Wasu yan bindiga dadi da ba a san kosu wanene ba, a jihar Rivers dake a Nigeria, sunyi garkuwa da wani dan kasar Lebanon, a yayin da yake kann hanyar sa ta zuwa aiki.

Ya zuwa yanzu dai mutane fararen fatu dake aiki a kamfaninnikan hakar mai, wadanda akayi garkuwa dasu a tsawon kwanaki goma da suka gabata sun kai 15.

To sai dai daga cikin su an sako guda tara, amma ragowar ciki har da jamusawa biyu , har yanzu ana ci gaba da garkuwa dasun.

Garkuwa ta baya bayan nan da akayi da dan kasar ta Lebanon dake aiki, a wani kamfanin gyare gyare, tazo ne a dai dai lokacin da , Jami´an tsaro a kasar, suka kaddamar da gagarumin shirin dakile fitinar tsagerun na Niger Delta, dake ci gaba da tashin zaune tsaye a yankin.

Yankin na Niger Delta dai , yanki ne da yayi kaurin suna wajen fuskantar tashe tashen hankula da kuma yawaitar yin garkuwa da fararen fatu ,dake aiki a kamfaninnikan hakar mai a yankin.