Tsamin dangantakar Saudiyya da Masar
April 29, 2012Ƙasar Saudiyya ta janye jakadanta, kana ta rufe ofishin jakadancin ta dake ƙasar Masar. Kamfanin dillalcin labaran Saudiyya ya ruwaito cewa an dau matakin ne don dalilan tsaro, inda masu bore suka kewaye ofishin jakadanci Saudiya a birnin Alƙahira, a martani bisa tsare wani Lawya ɗan ƙasar Masar wanda Saudiyya ta yi a lokacin da ya je yin Umrah. Wani kakakin gwamnatin Saudiyya yayi tir da masu boren, wadanda aƙalla suka kai dubu daya da suka yi dafifi a gaban ofishin jakadancin, kuma yace sun sun nufi kutsawa ciki.
Shugaban gwamnatin sojin Masar ya maida martani inda yace yana kan war-ware matsalar da taso. Saudiyya dai ta tsare Lawyan dan ƙasar Masar bayan da ya furta cewa yakamata a kafa mulkin demokraɗiyya, inda nemi yan Saudiyya suma sun yin boren ganin bayan mulkin kama karya tamkar na yan Masar, abinda gwamnati Saudiyya ta yi Allah wadai da shi.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Abdullahi Tanko Bala