Zafi ya halaka mutane 25 a Indiya
May 3, 2022Talla
Kasar Indiya ita ce kasa ta biyu a duniya wajen samar da alkama, amma yanayin zafi na shirin durkushe harkokin noma a bana sakamakon karancin ruwan sama da ake fuskanta sakamakon sauyin yanayni da kasar ke fuskanta tsawon shekaru biyar a jere. A watan Maris na shekarar 2022, kasar Indiya ta fara fuskantar tsananin zafi daga maki 33.1 a ma'aunin celsius zuwa sama da maki 40 a wasu yankunan kasar. Yanzu haka dai masana na gargadin cewa akwai yuwar zafin zai shafi lafiyar mutane da dama a yankunan da suke fuskantar tsanani zafi a kasar.