1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An kama masu adawa da matakan Corona

Gazali Abdou Tasawa
April 21, 2020

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun kama masu zanga-zangar adawa da matakan yaki da Coronavirus sama da 100 tare da iza keyar wasu guda 10 a gidan kurkuku na Koutoukale mai tsananain matakan tsaro.

https://p.dw.com/p/3bDcX
Gefängnis Koutoukale im Niger
Hoto: DW/A. Mamane

A Jamuriyar Nijar 'yan sanda sun kame wasu mutane 108 a lokacin wata zanga-zangar da suka gudanar a Yamai babban birnin Kasar tsakanin ranaikun 17 zuwa 19 ga wannan watan na Afrilu domin nuna rashin amincewarsu da dokar hana yawon dare da ta hana jam'i a masallatai wacce hukumomin kasar suka kafa domin yaki da yaduwar annobar cutar Coronavirus.

Kamafanin dillancin Labaran Faransa na AFP ya ce tuni ma dai Hukumomin kasar ta Nijar sun iza keyar wasu mutane 10 daga cikin wadanda aka kama zuwa babban gidan kurkuku mai tsattsauran matakan tsaro na garin Koutoukale da ke nisan kilomita 60 daga birnin Yamai.

Kwanaki uku ne dai a jere a kowane dare ake dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaro da mazaunan wasu unguwannin birnin na Yamai wadanda suka tayar da tarzoma tare da kone-konen tayoyi domin nuna adawarsu da matakan da hukumomin kasar suka dauka na neman hana yaduwar annobar Corona a kasar baki daya. Ya zuwa yanzu dai cutar ta harbi mutane 655, kana ta halaka mutane 20 a kasar ta Nijar