1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Kara tsaro a majalisar dokoki

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 10, 2021

Bayan da magoya bayan shugaban Amirka mai barin gado Donald Trump suka mamaye tare da kutsa kai cikin ginin majalisar dokokin Amirkan a ranar Larabar da ta gabata, majalisar dokokin Jamus ta tsaurara tsaro a harabarta.

https://p.dw.com/p/3nkaZ
Deutschland Berlin | Proteste gegen Coronamaßnahmen
Jami'an 'yan sanda a harabar majalisar dokokin JamusHoto: Fabrizio Bensch/REUTERS

Za dai a iya cewa, abin da ya faru a harabar majalisar dokokin Amirkan ya sanya majalisar dokokkin Jamus din ta Bundestag yin abin nan da masu magana kan ce daga na gaba ake ganin zurfin ruwa ko kuma in gemun dan uwanka ya kama da wuta ka shafa wa naka ruwa, ta hanyar kara yawan jami'an 'yan sandan da ke tsaro ginin majalisar dokokin kasar ta Bundestag.

Shugaban majalaisar dokokin Jamus din ta Bundestag Wolfgang Schäuble ne ya bayyana hakan, cikin wata sanarwa ga 'yan majalisar da jaridar Bild am Sonntag ta wallafa, inda ya ce 'yan sandan Berlin fadar gwamnatin kasar sun kara tsaurara matakan tsaro a baki dayan harabar majalisar ta Bundestag.