1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona ta yadu zuwa kasashe 195

Zainab Mohammed Abubakar
March 24, 2020

Kusan mutane dubu 400 ne suka kamu da cutar Coronavirus a yayin da wasu sama da dubu 17 suka rasa rayukansu a sassa daban daban. Banda Chaina, COVID-19 ta yadu zuwa kasashe 195.

https://p.dw.com/p/3ZyoX
Coronavirus in Indonesien Sumatra Menschen im Zug
Hoto: AFP/A. Qodir

Wani sakamakon bincike da ya fito yau Talata na nuni da cewar, killace wadanda suka harbu, nisanta juna a wuraren aiki da inda jama'a ke haduwa da rufe makarantu, sun kasance matakai masu inganci wajen yaki da yaduwar cutar COVID-19, bisa la'akari da martanin kasar Singapore kan wannan cuta mai kisa.

Masu bincike daga jami'ar Singapore sun ga yadda nisanta juna tsakanin mutane uku a lokaci guda, ya yi tasiri wajen rage yaduwar Corona tsakanin al'ummar kasar.