1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsawaita dokar ta-ɓaci a Najeriya

Usman ShehuMay 14, 2014

Shekara guda ke nan da kafa dokar ta ɓaci a yankin arewa maso gabashin Najeriya, shugaba Goodluck Jonathan ya gabatar da buƙatar ƙara wa'adin dokar ga majalisun dokokin ƙasar.

https://p.dw.com/p/1Bzdc
Goodluck Jonathan Präsident Nigeria Fernsehansprache ARCHIV
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Ƙasa da tsawon awoyi 24 da miƙa buƙatar neman ƙara tsawaita dokar ta-ɓacin a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe da shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya yi,an fara samun martani daga shugabannin al'ummar yankin da suka ce ba za ta saɓu ba wai bindiga a cikin ruwa.

Al'ummar Najeriya na nuna adawa da dokar ta-ɓacin

Kama daga gwamnatoci na jihohin uku da dokar ta kai ga shafa ya zuwa wakilansu da ke nan a majalisun tarrayar ƙasar biyu dai ra'ayi yana shirin zama guda game da adawa da sabuwar dokar. Kuma har ya zuwa yau 'yan majalisun ba su sanya ranar tattaunawa ba a kan dokar

Nigeria Polizei Polizisten auf Patrouille in Bauchi
Hoto: Getty Images/AFP

Zargin 'yan majalisun yanki arewacin ga gwamnatin da haɗa baki da Boko Haram

Tuni 'yan majalisun da suka fito daga yankin suka ce sabuwar dokar na daɗa tabbatar da hasashen haɗa baki a tsakanin mahukuntan ƙasar da ke Abuja da 'Yan Ƙungiyar Boko Haram, da nufin ci-gaban zarafin al'ummar yankin a faɗar Senata Ahmed Zanna da ke zaman ɗaya a cikin 'yan majalisar dattawan ƙasar daga Borno.

Alhaji Kashim Shettima
Hoto: DW/U. Musa

"Shugaban ƙasar shi ne wanda yakamata ya tsare mutane daga wannan hare-haren bai yi ba cikin shekaru uku, kuma har ya zo ya saka dokar ta-ɓaci a cikin shekarar da ta wuce."

Daga ƙasa ya a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahoton da wakilinmu na Yola za aiko mana dangane da ra'ayoyin jama'a, da kuma hira da Ahmed Salisu ya yi da Barr. Waziri Yusha'u Mamman, masanin kudin tsarin mulkin Najeriya

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Abdourahamane Hassane