Tsawaita takunkumin dokar Trump kan baki
March 30, 2017Talla
Derrick Watson ya kuma bayyana cewa zai mayar da wannan mataki nasa daga na wucan gadi zuwa na har abada.
Kuma baban antoni janar na kotun jihar ta Hawai ya sanar da cewa matakin da alkali Derrick Watson ya dauka a halin yanzu, mataki ne da a idon doka na iya haramta wa gwamnatin Donald Trump gudanar da duk wata kwaskwarima ga dokar ta baki da 'yan gudun hijira.
Makonni biyu da suka gabata ne dai alkalin babbar kotun jihar ta hawai Derrick Watson ya dauki mataki saka takunkumi ga wannan doka ta Shugaba Trump wacce ta tanadi haramta wa 'yan asalin wasu kasashe shida akasarinsu na Musulmi shiga kasar ta Amirka.